Isa ga babban shafi

Napoli ta kara farashin Victor Osimhen

Kungiyar Napoli da ta yi nasarar lashe gasar Serie A, ta kara farashin dan wasan gabanta Victor Osimhen, bayan taimaka mata da ya yi wajen lashe gasar a karon farko a cikin shekaru 33. 

Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen
Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen AP - Fabio Ferrari
Talla

Jaridar Matino da ake wallafawa a kasar ta ce a yanzu kungiyar ta ce kudin sa sunan tayin dan wasan ya tashi daga Euro 150 zuwa 160. 

Akwai dai manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai irin su Bayern Munich da PSG da Arsenal da Chelsea da kuma Manchester United ke rige-rige wajen dauko dan wasan. 

Duk da dai shugaban kungiyar ta Napoli Aurelio de Laurentiis ya ce dan wasan ba na saidawa bane, amma kuma tana neman yin kasuwanci da dan wasan na gaba. 

A yanzu dai dan wasa ne ke kan gaba wajen yawa jefa kwallo a raga a gasar Serie A a kakar wasan bana, inda ya jefa kwallaye 23 daga cikin wasanni 27 da yayi a gasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.