Isa ga babban shafi

United ta sha gaban Chelsea a kokarin dauko Osimhen daga Napoli

Rahotanni na cewa Manchester United ta sha gaban Chelsea a yunkurin dauko dan wasan Napoli Victor Osimhen a kasuwar musayar 'yan wasa ta bana.

Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen,15/03/23
Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen,15/03/23 © Gregorio Borgia/AP
Talla

Man United da Chelsea dukkaninsu na zawarcin dan wasan na Najeriya, haka su ma Bayern Munich da Paris Saint-Germain duk na zawarcin dan wasan mai shekaru 24.

A cewar Football Insider, Man United na kan gaba da Chelsea a tseren, saboda ana ganin zai yi wuya Blues ta iya biyan farashin da Napoli ta sa kan dan wasan.

Chelsea zata bukaci siyar da ’yan wasa da dama a wannan bazarar domin gudun wuce ka’idar kudin da zata iya kashewa saboda yadda ta yi ta kashe kudi a baya.

Dan wasan na Najeriya ya taka rawar gani sosai a kungiyarsa ta Italiya a kakar wasa ta 2022-23, inda ya zura kwallaye 26 sannan kuma ya taimaka aka zura kwallaye biyar a wasanni 32 da ya buga a dukkan gasa.

Osimhen ya zura kwallaye 21 a gasar Seria A wannan kakar, tare da kasancewarsa mai taka rawar gani a kungiyar Naples tana da maki 17 tsakaninta da Lazio mai matsayi na biyu a saman tebur.

Har yanzu Osimhen na da sauran shekaru biyu kafin  kwantiraginsa da Napoli ta kawo karshe, sai dai ana ta cece-kuce game da makomarsa a kungiyar gabanin bude kasuwan ‘yan wasa ta bazara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.