Isa ga babban shafi

Juventus ta buga wasan farko bayan zaftare mata maki 15 a Seria A

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta kasar Italiya ta koma ta 9 a gasar Seria A, bayan wasan da ta fafata da Atlanta, wanda suka tashi 3-3.

'Yan wasan kungiyar Juventus
'Yan wasan kungiyar Juventus REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Wasan dai shi ne na farko da Juventus ta buga tun bayan da hukumar kwallon kafa Italiya ta zaftare wa kungiyar maki 15, saboda samun ta da laifin bayar da lissafin karya kan hada-hadar kudade da musayar ‘yan wasa.

A baya Juventus na da maki 37 ne a matsayi na 4 a gasar Seria A, sai dai bayan rage mata maki 15 kuma ta koma ta 10.

A ranar Lahadi kuma ta matsa zuwa matsayi na 9, bayan samun maki  guda a wasan da ta buga 3-3 da Atlanta.

Yayin da  ya rage wasanni 20 a kammala kakar wasa ta  bana, wasu na ganin zai yi wahala Juventus ta iya samun damar buga gasar cin kofin zakarun Turai mai zuwa, ta hanyar kammala kakar wasa ta  bana a matakin kungiyoyin hudu na farko a gasar Seria A.

Daga cikin tuhume-tuhumen da masu gabatar da kara ke yi wa Juventus akwai, saba ka’ida wajen musayar ‘yan wasan da ta yi da Barcelona a shekarar 2020, inda dan wasanta na tsakiya Miralem Pjanic ya koma Barcelonan, yayin da ita kuma ta karbi Arthur Melo.

Masu gabatar da kara a Italiyan kuma sun bankado wasu bayanan sirri da ke nuna cewar, Juventus din ta rika biyan Cristiano Ronaldo wasu makudan kudade a boye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.