Isa ga babban shafi

Mourinho ya kusa dukan alkalin wasa

Jami’an da ke taimakawa Jose Mourinho sun yi da gaske kafin hana shi afkawa alkalin wasa da duka, inda daga bisani alkalin ya kore shi daga fili a wasan da AS Roma ta sha kashi a hannun Atalanta da ci 1-0 a ranar Lahadi.

Jose Mourinho.
Jose Mourinho. Action Images via Reuters - LEE SMITH
Talla

Mourinho mai shekaru 59 ya shiga filin wasa ne domin fuskantar alkalin wasa saboda hana su damar bugun fanaretin da yake ganin kungiyarsa ta cancanci a ba ta.

Lamarin ya samo asali ne bayan da ake zargin Caleb Okoli na Atlanta da yi wa Nicolo Zaniolo keta a cikin dairar yadi na 18 a minti na 54 da fara wasa, amma a maimakon baiwa Roma damar Bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai alkalin wasa Daniele Chiffi ya baiwa Atlanta damar bugun tazara.

Bayan korar Mourinho daga fili dai magoya bayan AS Roma sun rika rera wakar goyon bayan kocin nasu domin kara masa kwarin gwiwa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da alkalin wasa yake baiwa Jose Mourinho jan kati tare da korarsa daga filin wasa ba, saboda ire-iren zafafan martanin da kocin kan maida a duk lokacin da bai gamsu da matakan da aka dauka kan 'yan wasa ko kungiyar da yake horaswa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.