Isa ga babban shafi

Mourinho ne ya fara lashe gasar Turai ta Conference League

Jose Mourinho ya zama na farko da ya lashe sabon kofin gasar Turai da ake kira da Conference League. Ya samu manyan nasarori a aikinsa na kocinta, amma nasarar da Roma ta samu a gasar cin Europa Conference League ya sa shi zubar da hawaye bayan da ya taimakawa kulob din na Italiya lashe manyan kofin Turai na farko.

Kocin Roma José Mourinho da tawagarsa bayan lashe gasar Conference League.
Kocin Roma José Mourinho da tawagarsa bayan lashe gasar Conference League. © AFP - OZAN KOSE
Talla

Sabuwar Gasar itace ta uku a Turai, amma Mourinho na ganin na da mahimmanci tamkar lashe gasar zakarun Turai biyu da yayi a baya wato da Porto a 2004 da kuma Inter Milan a shekarar 2010.

Mourinho ya zama koci na farko da ya lashe dukkanin manyan gasannin Turai guda uku bayan ya samu nasara a wasannin Turai biyar.

Roma ta lashe kofin ne, bayan da ta yi nasara a kan Feyenoord Rotterdam da ci 1-0, jiya a Albania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.