Isa ga babban shafi
Europa Conference League

Mourinho ya fashe da kuka bayan nasarar Roma ta zuwa wasan karshe

Jose Mourinho ya fashe da kuka bayan da kungiyarsa AS Roma ta kai wasan karshe na gasar Europa Conference League bayan doke Leicester ci 2 – 1 gida da waje.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho.
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho. AFP
Talla

Kwallon daya mai ban haushi da Tammy Abraham ya zura a mintuna na 11 da soma wasa ya baiwa kungiyar Jose Mourinho nasara.

Dan wasan gaba na AS Roma Edin Dzeko (R) ya zura kwallaye biyu a ragar Benevento.
Dan wasan gaba na AS Roma Edin Dzeko (R) ya zura kwallaye biyu a ragar Benevento. AFP

Mourinho mai shekaru 59 da yace wannan tamkar nasara ce a gasar zakarun Turai, yace nasarar ta sama da magoya baya sama da dubu 70 da suka cika filin wasa na Olimpico a daren Alhamis.

Kulob din na Italiya zai kara da Feyenoord a wasan karshe na farko a ranar 25 ga watan Mayu a Tirana, na kasar Albania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.