Isa ga babban shafi
Europa

Besiktas ta yi waje da Liverpool a Europa

Hankalin Liverpool yanzu zai dawo a wasanninta na gida a Ingila bayan Besiktas ta yi waje da ita a gasar Eurapa League a bugun fanariti. Beskitar ta rama kwallon da Liverpool ta zira ne a karawa ta farko.

'Yan wasan Liverpool na Ingila
'Yan wasan Liverpool na Ingila REUTERS/Phil Noble
Talla

Dejan Lovren ne ya barar wa Liverpool da fanariti bayan an kammala lokacin wasan, kungiyoyin biyu na da jimillar kwallaye 1 da 1.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce yanzu hankalinsu zai dawo gida ne a Ingila domin ganin yadda zata kaya musamman haduwar Liverpool ta Man City a ranar Lahadi a Premier League.

Mai rike da kofin gasar Sevilla ta tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta doke Borussia Moenchengladbach da jimillar kwallaye ci 4 da 2.

Fiorentina ta yi waje ne da Tottenham da ke shirin haduwa da Chelsea a karshen mako.

Everton ce kungiya tilo daga Ingila da ta samu nasarar haurawa zuwa gaba a gasar Europa League bayan ta lallasa Young Boys ta Swiss da jimillar kwallaye 7 da 2.

Roma ta sha da kyar ne a hannun Feyenoord inda sau biyu alkalin wasa na dakatar da wasan saboda wariyar launin fata da aka nunawa dan kasar Cote d’Ivoire Gervinho. ‘yan kallo sun ta jifarsa da ayaba a gidan Feyenoord.

Inter ta tsallake ne bayan ta doke Celtic da jimillar kwallaye 4-3.

Kungiyoyin Italiya biyu, Napoli da Torino dukkaninsu sun tsallake a gaba bayan sun yi waje da Trabzonspor da Athletic Bilbao.

Zenit Saint-Petersburg ta yi waje da PSV Eindhoven, kamar yadda Ajax a Legia Warsaw.

Dinamo Moscow da Dynamo Kiev dukkaninsu sun tsallake bayan sun doke Anderlecht and Guingamp.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.