Isa ga babban shafi
Wasanni

Cinikin Neymar ya sa Manajan Barca ajiye mukamin shi

Shugaban kungiuyar kwallon kafa ta Barcelona Sandro Rosell, da ke fuskantar shari’a saboda sayen shahararren dan wasan kasar Brazil Neymar, ya ajiye mukamin. Sandro Rosell ya rike kungiyar, har tsawon shekaru 3 da rabi, kuma a halin yanzu itace ke rike da kofin La ligan kasar Spain.An fara matsin lamba kan Rosell, mai shekaru 49, bayan wani alkali ya amince ya saurari karar da wani masoyin kungiyar ya shigar kan shi.Mutumin na zargin manajan da almbazzaranci da kudaden jama’a, sakamakon cinikin da ya kulla kan sayen Neymar a shekarar bara.Yanzu mataimakkin shugaban kungiyar, Josep Maria Bartomeu zai maye gurbin Rosell har zuwa lokacin da wa’adin su zai kare a shekarar 2016.Sai dai fa Rosell ya dage kan cewa shi bai aikata ba daidai ba kan cinikin, da Barca ta kashe fiye da EURO Miliyon 57, wato Dalar Amurka miliyon 77 kan dan wasan. 

dan wasan kungiyar Barcelona, Neymar
dan wasan kungiyar Barcelona, Neymar REUTERS/Albert Gea
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.