Isa ga babban shafi
La liga

Clasico: Neymar da Bale za su yi haskawar farko

A bana akwai Neymar na Barcelona da Gareth Bale na Real Madrid sabbin tsadaddun ‘Yan wasa da zasu fara haskawa a karawar adawa tsakanin Barcelona da Real Madrid a gobe Assabar.

Wasan Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid da za'a fafata a ranar Assabar
Wasan Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid da za'a fafata a ranar Assabar
Talla

Tazarar maki uku ne Barcelona da Atletico Madrid suka ba Real Madrid a teburin La liga.

Amma a karshen makon jiya Barcelona ta yi hasarar maki biyu bayan Osasuna ta rike ta babu ci kamar yadda AC Milan ta rike Barcelona ci 1-1 a gasar zakarun Turai a filin wasa na San Siro.

Amma a karshen makon jiya Real Madrid ta doke Malaga ne ci 2-0, tare da lallasa Juventus ci 2-1 a gasar zakarun Turai a tsakiyar mako.

Kungiyar Atletico Madrid za ta yi fatar a tashi kunnen doki a Clasico domin samun tazara tsakaninta da Barcelona da Real Madrid amma idan ta lashe wasanta tsakaninta da Real Betis.

A bana dai Barcelona da Real Madrid zubin sabbin masu horar da ‘Yan wasa ne za su jagoranci wasan Clasico a ranar Assabar, Ancelotti da kuma Tata Martino, wadanda za su gaji adawa irinta Pep Guardiola da Jose Mourinho.

Sai dai kuma duk da zubin sabbin zarata irinsu Neymar da Bale amma har yanzu ido zai koma ne ga Messi da Ronaldo wadanda suka jima suna adawa a Clasico.

10:24

Mogoya bayan Barcelona da Real Madrid sun tabka muharawa

Idan Messi ya kada kwallo a raga a Clasico zai kasance ya kafa wani tarihi a Barcelona a matsayin wanda yafi jefa kwallaye a ragar Madrid, wanda zai sha gaban di Stefano.

A wasannin Clasico 7 da aka buga kuma Ronaldo ya jefa kwallaye 6 a ragar Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.