Isa ga babban shafi
Spain

Clasico: Real Madrid 1-1 Barcelona

Barcelona da Real Madrid sun tashi kunnen doki ci 1-1 a Santiago Bernabeu a karawar farko na gasar Copa Del Ray zagayen kusa da karshe. Nan da makwanni uku ne kungiyoyin biyu za su sake karawa a Nou Camp inda za’a fitar da gwani.

Dan wasan Real Madrid Xabi Alonso, hannun shi a fuskar Messi na Barcelona a wasan da suka yi kunnen doki ci 1-1 a Santiago Bernabeu
Dan wasan Real Madrid Xabi Alonso, hannun shi a fuskar Messi na Barcelona a wasan da suka yi kunnen doki ci 1-1 a Santiago Bernabeu REUTERS/Juan Medina
Talla

Fabregas ne ya fara zirawa Barcelona kwallo a ragar Madrid kafin daga bisani Raphael Varane ya barke wa Madrid kwallon a ragar Barcelona.

Za’a dai kwashe kusan tsawon makwanni uku kafin kungiyoyin biyu su sake karawa, amma nan da makwanni biyu ne kuma Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester United a Santiago Bernabeu.

A yau ne Atletico Madrid za ta kara da Sevilla.

Babu wanda ya zira kwallo a raga tsakanin Messi da Ronaldo inda a wasanni 10 na baya baya nan, Messi ya zira kwallaye 16, Ronaldo kuma ya zira kwallaye 12. Amma kwallaye Hudu da Messi ya zira a ragar Osasuna ya sa dan wasan ya samu jimillar kwallaye 33 a La liga, Amma Ronaldo yana da kwallaye 21 ne bayan zira kwallaye uku a ragar Getafe.

Da Messi ya zira kwallo da zai kasance ya yi kafada da kafada da Di Stefano, tsohon dan wasan Barcelona wanda ya zira kwallaye 18 a ragar Real Madrid a wasan Clasico.

Wannan ne karo na Hudu da manyan kungiyoyin biyu na Spain suka kara a kakar bana.

Real Madrid ce ta lashe kofin Super Cup bayan samun yawan kwallaye a gidan Barcelona, Kuma a La liga a bana kungiyoyin biyu sun tashi ne ci 2-2 a Nou Camp.

Sai dai a bana tazarar maki 15 ne Barcelona ta ba Real Madrid a Teburin La liga.

Kwallayen da Messi ya zira a raga a ranar Lahadi, shi ne ya ba shi damar kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya zira kwallaye a wasanni 11 a jere da jere.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.