Isa ga babban shafi
La liga

Casillas da Ramos sun karyata zargin sun bukaci a sallami Mourinho

‘Yan wasan Real Madrid Iker Casillas da Sergio Ramos sun karyata zargin cewar sun nemi Real Madrid ta sallami Mourinho, wannan kuma ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin ‘Yan wasan da kocinsu kamar yadda aka ruwaito.

Kocin Real Madrid Jose Mourinho a filin wasa na Santiago Bernabéu.
Kocin Real Madrid Jose Mourinho a filin wasa na Santiago Bernabéu. © Reuters
Talla

A ranar Talata ne Jaridar Marca da ke goyon bayan Madrid ta ruwaito labarin cewar Casillas da Ramos sun bukaci a sallami Mourinho tare da barazanar ficewa kungiyar idan har Real Madrid ba ta sallame shi ba.

Sai dai kuma Casillas da Ramos sun fito sun karyata rahoton tare kare Mourinho daga zargin yana fuskanta matsala da ‘Yan wasan shi.

Copa Del Ray

Barcelona ta tsallake zagayen kusa da karshe a gasar Coper Del Ray bayan doke Malaga da jimillar kwallaye ci 6-4, Bayan a karawar farko kungiyoyin biyu sun tashi wasa ci 2-2.

A zagayen kusa da karshen Barcelona za ta kara ne da Real Madrid, a yayin da kuma Atletico Madrid ta kece raini da Sevilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.