Isa ga babban shafi
La liga

Barcelona ta ci ribar Neymar bayan doke Madrid

Gareth Bale tsadadden dan wasan duniya ya samu damar haskawa a babban wasan Clasico tsakanin Real Madrid da Barcelona amma Neymar ya dushe sunansa sabon matashin dan wasa da ya fara haskawa a bana a wasan Clasico.

Dan wasan Barcelona Neymar yana murnar zira kwallo a ragar Real Madrid a wasan Clasico
Dan wasan Barcelona Neymar yana murnar zira kwallo a ragar Real Madrid a wasan Clasico REUTERS/Albert Gea
Talla

Neymar ne ya fara zirawa Barcelona kwallo a raga kafin daga bisani Alexis Sanchez ya sake jefa kwallo ta biyu.

Ana mintinan karshe Jese Rodriguez ya samu sa’ar jefa kwallo a ragar Barcelona wanda ya sa aka tashi wasan ci 2-1.

Carlo Ancelotti ya cire Bale wanda Real Madrid ta dankarawa makudan kudade saura minti Talatin a kammala wasa ya sako Karim Benzema.

Bayan kammala wasan Neymar ya bayyana farin cikinsa musamman kwallonsa da ya zira a raga a babban wasan Clasico.

Barcelona ta yo cefanen Neymar ne akan kudi euro Miliyan 57 daga Kungiyar Santos ta Brazil, kusan rabin kudin da Real Madrid ta saye Bale.

Sai dai kuma kocin Madrid Carlo Ancelotti ya kare Bale yana mai cewa dan wasan yana bukatar lokaci kafin ya girgije wanda tun zuwansa kwallo guda ya zira a raga a wasansu da Villareal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.