Isa ga babban shafi

Dan wasan Barcelona Guiu ya zura kwallo mai ban mamaki a wasansa na farko

Marc Guiu ya ci kwallon da ta bai wa Barcelona nasara a kan Atletico Bilbao da ci 1 da nema a gida, dakikoki 33 bayan da ya shiga filin wasa a wasansa na farko da ya fara bugawa kungiyar. 

Matashin dan wasan kungiyar Bercelona Marc Guiu
Matashin dan wasan kungiyar Bercelona Marc Guiu © AFP
Talla

Dan wasan gaban mai shekaru 17, wanda dan kasar Spaniya ne ya shiga filin wasan ne a minti na 79 bayan da aka cire matashin nan, wato Fermin Lopez, kuma ba tare da bata lokaci ba ya runtuma kwallo a raga. 

Hakan naa nufin ya ci kwallonsa ta farko a gasar La Ligar da ya buga wa Barcelona, kuma kwallo mafi sauri a tarihin kungiyar. 

Wannan nasarar ta kai Barcelona matsayi na 3 a teburin gasar La Liga na wannan kaka, kuma tazarar maki guda  ne kawai tsakaninta da Real Madrid da ke ta daya a teburin. 

Tuni dai ‘yan wasa da masu sharhi kan harkokin wasanni suka fara karin haske kan rawar da yaron ya taka da kuma irin yadda ya kamata mai horas da kungiyar yayi amfani da shi, ta yadda za’a a moreshi, yayin da ake ganin tuni tauraruwar yaron ta fara haskakawa da wannan kwallo da ya ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.