Isa ga babban shafi

Wata gobara da ta tashi a gidan rawa ta kashe mutane 13 a Spaniya

Wata gobara da tashi a  gidan rawa da ke yankin Murcia na kasar Spaniya ta yi sanadin mutuwar mutane 13, yayin da ake fargabar adadin ka iya karuwa.

Gidan rawar na cikin gidajen rawar da aka fi samun rahoton tashin gobara a kasar
Gidan rawar na cikin gidajen rawar da aka fi samun rahoton tashin gobara a kasar AFP - LE PHU
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa bayan da wutar ta kama kuma sai ginin ya rufta kan jama’ar da ke cikin gidan rawar.

Wutar wadda har yanzu babu tabbaci kan dalilin tashin ta ta ratso ne daga wani gidan rawar da babu kowa a cikin sa ta kuma shiga inda mutane ke tsaka da holewa.

Hukumar kashe gobara ta kasar ta ce har yanzu masu aikin ceto na ci gaba a laluben mutanen da baraguzan gine-gine suka danne.

Magajin garin Murcia Jose Ballesta ya shaidawa manema labarai cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiya agogon kasar, kuma nan take ta yi karfin da aka kasa shawo kanta cikin gaggawa.

Ballesta ya kuma ci gaba da cewa har kawo yanzu ana ci gaba da aikin neman mutane cikin barguzan gine-gine, yayin da ake fargabar sauran ginin gidan rawar da ke tsaye zai iya ruftawa a kowanne lokaci.

Babban sufeton ‘yan sandan kasar Diego Seral ya ce gidan rawar da wutar ta tashi mai suna Fonda Club na cikin manyan gidajen rawa uku da kasar ke takama da su, kuma wanda ya fi kowanne tarihin tashin gobara.

Yace rushewar da ginin yayi shine babban dalilin da ya sa har yanzu ba’a kai ga tattara alkalman mutanen da suka mutu ba, saboda akwai yakinin cewa za’a iya samun mutanen a kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.