Jamus ta fitar da kanta daga jerin kasashe masu karfin nukiliya
Jamus ta kashe na’urorin inganta makamashin nukiliyarta 3 da suka saura a kokarin da take na daina amfani da makamashi mai gurbata muhalli, tare da lalubo mafita a game da karancinsa da yakin Ukraine ya haddasa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A yayin da akasarin kasashen yamma ke kokarin kara kudaden da suke kashewa a bangaren makamashin nukiliya, Jamus ta kawo karshen amfani da wannan makamashi tun da wuri.
Jim kadan bayan karfe 12 na daren Asabar, kamfann RWE mai kula da makamshin a kasar ya fitar da wata sanarwar da ke cewa an kashe wadannan na’urori.
Tun a shekarar 2002 kasar da ta fi karfin arziki a nahiyar Turai ta fara tunanin yin watsi da makamashin nukiliya, amma a shekarar 2011 gwamnatin Angela Merkel ta kara azama a game da shirin, biyo bayan hatsarin tashar nukiliyar Fukushima a Japan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu