Isa ga babban shafi

Putin na barazanar amfani da kwarya-kwaryar makamin nukiliya a yakin Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce zai  aike da kanana makaman nukiliya a makwafciyar kasar, Belarus, abin da ke nufin cewa makaman za su kasance daf da hanyoyin shiga Tarayyar Turai.

Shugaban Rasha Vladimir
Shugaban Rasha Vladimir AP - Gavriil Grigorov
Talla

 A baya, Putin ya sha yin kashedin cewa yana iya amfani da makaman nukiliya Ukraine idan ya fuskanci Rasha na fuskantar barazana, lamarin da ke farafado da zamanin yakin cacar  baka.

Ya kuma ce  zai jibge gurbatacen makamshin Uranium idan har aka bai wa Ukraine   gudummawar makamamashin daga yammacin Turai, biyo bayan sanarwar Birtaniya da ta nuna haka.

A kan ko wane irin martanin Rasha za ta mayar idan kasashen yamma suka sama wa Ukraine dagwalar karfen uranium biyo bayan sanarwar Birtaniya,  Putin ya ce  Rasha tana da ita bila adadin.

Kungiyuar da ke fafutukar  neman kawo karshen makaman nukiliya a duniya, ICAN ta yi gargadin cewa barazanar da ake yin  amfani da makamin nukiliya ko dangoginsa tana fadada yiwuwar amfani da shi.

Dagawalar karfen uranium dai ana samun ta ne a yayin tace uranium kansa, kuma  ba shi da hatsari har na kashi 60 idan aka kwatanta da danyen uranium, tana kuma da hatsari ga sojojin da ke amfani da  ita, daa kuma aal’ummar da ke yankin da aka yi amfani da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.