Isa ga babban shafi

Rasha ta amince da tattaunawa kan makomar tashar nukiliya ta Zaporizhzhia

Shugaba Vladmir Putin ya shaidawa hukumar da ke sanya idanu kan nukiliya ta Duniya IAEA cewa a shirye Rasha ta ke ta shiga tattaunawa game da makomar tashar nukiliyar Ukraine ta Zaporizhzhia, mafi girma a nahiyar turai da yanzu ke karkashin ikon Moscow da nufin ba ta cikakkiyar kariya.

Ganawar shugaba Vladimir Putin da shugaban hukumar AIEA Rafael Grossi.
Ganawar shugaba Vladimir Putin da shugaban hukumar AIEA Rafael Grossi. AP - Pavel Bednyakov
Talla

Yayin wata zantawar Putin da shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi jiya talata a birnin Saint Petersburg, shugaban ya ce Rasha ta shirya tsaf don fara tattaunawa da nufin cimma jituwa kan tashar nukiliyar ta Zaporizhzhia amma bisa tarin sharudda.

Tattaunawar ta Putin da Grossi na zuwa ne kwanaki kalilan bayan tashar ta Zaporizhzhia ta koma karkashin ikon Rasha kasancewarta a guda cikin yankunan Ukraine 4 da Moscow ta mamaye tare da mayar da su mallakinta, lamarin da ya sanya fargaba kan makomar tashar da ke matsayin mafi girma a nahiyar Turai.

Shugaban Hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya ce zai yi ganawar gaggawa da Volodymyr Zelensky na Ukraine bayan ganawar ta sa da Putin a jiya da nufin samar da cikakken tsaro ga tashar wadda ke fuskantar barazana dai dai lokacin da bangarorin biyu ke ci gaba da gwabza yaki.

Grossi na ci gaba da kai kawo tsakanin kasashen biyu na Rasha da Ukraine, da nufin samar da sauki ga rudanin da Duniya ta shiga musamman kasashen yammaci game da ci gaba da kasancewar tashar ta Zaporizhzhia a karkashin ikon Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.