Isa ga babban shafi
Faransa-Fina-finai

Fitaccen jarumin fina-finai Belmondo ya rasu

Shahrarren mai shirya wasan sinima na kasar Faransa Jean-Paul Belmondo ya rasu a wannan Litinin a gidansa da ke birnin Paris yana da shekaru 88 a duniya.

Jean-Paul Belmondo
Jean-Paul Belmondo Joel Saget AFP/Archivos
Talla

Belmondo, wanda aka haifa a 1933, daya ne daga cikin shahrarrun masu fitowa a fina-finai a farkon shekarun 1970, kuma kafin rasuwarsa ya shirya fina-finai akalla 80 da aka fassara cikin harsuna daban-daban na duniya.

Wasu daga cikin fina-finansa da suka yi fice sun hada da "A bout de souffle", "Le Guignolo" da dai sauransu, fina-finan da wasu daga ciki ke kasancewa na nishadi da kuma camama don faranta ran masu kallo, yayin da mafi Faransawa ke kiran sa da suna Bebel ko kuma Le Magnigifique sakamakon yadda yake daukar kasada a cikin fina-finansa.

Lauyan Jean-Paul Belmondo Michel Godest, ya ce marigayin ya rasu ne bayan share dogon lokaci yana jinya da kuma nuna alamun gajiya.

Alkalumma dai sun tabbatar da cewa a tarihi, an sayar da tikitin shiga sinima fiye da milyan 130 don kallon fina-finan Belmondo a cikin shekarun da suka gabata.

A 2010, Belomondo ya samu kyautar yabo da ake kira Film Critics Association a birnin Los Angeles na Amurka, kafin ya sake lashe kyautar gasar fina-finai mafi girma a duniya wato Cannes Film Festival a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.