Isa ga babban shafi
Faransa

Agnès Varda Mashahuriya mai sana’ár fina- finai ta rasu

Mashahuriya mai sana’ár fina finan nan yar kasar Faransa uwargida Agnès Varda ta cika a daren jiya alhamis kawo safiyar yau jumaá bayan da ta share shekaru 90 a duniya kamar yadda iyalanta suka sanar da kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP.

Agnes Varda
Agnes Varda REUTERS/Regis Duvignau/File Photo
Talla

Uwargida Agnès dai na daga cikin mata masu shirya fina finai da suka shahara a faransa da ta shirya fim din Cleo de 5 a 7 a shekara ta 1962 "Les Glaneurs et la Glaneuse" ( a shekara ta 2000), "Les plages dAgnès (shekara ta 2009) ko kuma "Visages, villages" (shekara ta 2017).

A makon da ya gabata dai ne Agnes Varda ta samu ganawa da manema labarai na kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP a gidan ta dake tsakiyar Faransa.

Agnes Varda ta rasu bayan da ta yi fama da cutar Kansa na tsawon lokaci.

Ta rasu ta na mai shekaru 90 a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.