Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Ana shirin komawa tattauna samar da yarjejeniyar tsagaita buda wuta ta karshe a Gaza

Izraela da Palastinawa na ci gaba da shirin sake komawa wata sabuwar tattaunawa da zata fayyace ko za su tsawaita tsagaita buda wutar da suka cimma a yankin Gaza ko kuma a a  

AFP PHOTO / JEAN-CHRISTOPHE MAGNENET
Talla

A ranar litanin ne yarjejeniyar tsagaita wutar zata kawo karshe, bayan yakin tsawon wata guda da suka gwabza, mafi munin rikici da suka taba yi, wanda kuma ya salwantar da rayuka masu yawa, tun lokacin da Izraelar ta mamaye palestinawa a cikin shekarun 1960

A daidai lokacin da bangarorin 2 ke komawa teburin tattauna tsagaita buda wutar a Gazar A gobe lahadi, a yau assabar an shiga rana ta 6 a jere da tsagaita wuta, duk da cewa, an dan samu dan karamin tashin hankali, inda aka harba wasu yan rokoki a kan Izraela, a yayinda ita kuma Izraelar ta dan mayar da martanin da jiragen yakinta a daren laraba zuwa safiyar Alhamis a suka gabata

Rikicin wata gudan dai yayi sanadiyar rasa rayukan palestinawa 2000 a yayinda Izraela ta rasa mutane 70 kacal
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.