Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Kamaluddeen Garba kan dalilin da ke sanya likitocin Najeriya ficewa ketare

Wallafawa ranar:

Babbar kwalejin horar da likitoci ta duniya, wato ‘International College of Surgeons’ reshen Najeriya, ta ce likitoci dubu 6 da 221 ne suka koma aiki Birtaniya daga Najeriya a cikin shekaru 6 da suka gabata, saboda neman rayuwa mai inganci. 

Likitocin Najeriya ne kan gaba a sahun wadanda ke ficewa neman aiki ketare, sakamakon abin da suka ce gwamnati bata biya musu bukatunsu.
Likitocin Najeriya ne kan gaba a sahun wadanda ke ficewa neman aiki ketare, sakamakon abin da suka ce gwamnati bata biya musu bukatunsu. © daily post
Talla

Cibiyar horar da ma’aikatan lafiyar ta ce wannan rige rigen da likitoci ke yi na barin Najeriya, ya dada haifar da matsala da kuma sanya mutane sama da miliyan 40 basa iya ganin likita guda da zai duba halin lafiyarsu. 

Shugaban kwalejin, Farfesa Akanimo Essiet ya gabatar da wadannan alkaluma bayan kammala taron masanan kwalejin karo na 56, inda ya bayyana cewar matsalar ta yi matukar illa wajen rage yawan ma’aikatan lafiya a Najeriya. 

Essiet ya ce kafin shekarar 2022, likita guda ne ya ke kula da marasa lafiya dubu 4 a Najeriya, sabanin ka’idar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya wadda ta ce ana bukatar likita guda domin ya kula da marasa lafiya 600. 

Essiet ya ce an samu gibi sosai wajen jami’an da ke aikin kula da lafiya a Najeriya, yayin da adadin likitocin da ke aiki a Birtaniya ya tashi daga 4,765 a shekarar 2017, zuwa 10,986 a wannan shekarar. 

Dangane da dalilan da suka sa ma’aikatar lafiyar ke barin Najeriya zuwa Turai, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Kamaluddeen Garba, ‘dan Najeriya da ke aiki a Birtaniya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.