Isa ga babban shafi

Rasha da Nijar sun rattaba hannu kan karfafa yarjejeniyar tsaron da suka kulla

Kasar Rasha ta sanar da kulla sabuwar yarjejeniyar bunkasa huldar tsaro da Jamhuriyar Nijar, daya daga cikin kasashen da sojoji suka gudanar da juyin Mulki a yankin Sahel.

Wasu magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, dauke da tutar kasar Rasha a birnin Yamai.
Wasu magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, dauke da tutar kasar Rasha a birnin Yamai. AP - Sam Mednick
Talla

Wannan mataki na daga cikin yunkurin da kasar Rasha ta dade tana hankoro wajen bunkasa harkokin ta a nahiyar Afirka, amma matakin sai ya samu tasgaro a watan Yunin bara sakamakon boren da aka samu daga rundunar sojojin hayar Wagner da take amfani da ita. 

Mataimakan ministan tsaron Rasha Yunus-bek Evkurov da Alexander Fomin suka gana da ministan tsaron Nijar Salifou Modi a birnin Moscow inda aka kulla yarjejeniyar, yayin ziyarar aikin da Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine ya kai kasar. 

Yayin ganawar da bangarorin suka yi, ma’aikatar tsaron Rasha tace, sun amince da ci gaban huldar sojin dake tsakaninsu, yayin da suka sake duba wasu bangarorin da za’a inganta su. 

Kasashen biyu sun amince a tsakaninsu da su yi aiki tare wajen tabbatar da tsaro a Nijar da kuma inganta shirin ko-ta-kwana na sojin ta domin tinkarar duk wata barazana. 

A watan Disambar da ta gabata, tawagar ma’aikatar tsaron Rasha ta ziyarci Jamhuriyar Nijar, inda ta gana da shugabannin sojinta da suka gudanar da juyin Mulki a watan Yuni da kuma rattaba hannu a kan yarjejeniyar bunkasa hadin kan soji a tsakanin su. 

Jamhuriyar Nijar ta karkata akalar diflomasiyarta zuwa Rasha, bayan kawar da zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed wanda ke hulda kut-da-kut da Faransa, tare da soke yarjejeniyar hadin kan sojin dake tsakanin kasashen biyu, abinda ya kawo ficewar sojojin Faransa 1,500 dake yaki da’yan ta’adda a kasar. 

Sojojin dake mulkin Nijar sun sanar da soke yarjejeniyar soji da wasu kasashen Turai guda 2, yayin da suke maraba da zuwan Rasha. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.