Isa ga babban shafi
Rahoto kan sauyin yanayi

Yadda gobarar daji ta lalata abincin dabbobi a Nijar

Yayin da ake gudanar da taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Dubai na Hadeddiyar Daular Larabawa, a Jamhuriya Nijar, gobarar daji da ake fuskanta a kai a kai ta jefa al'ummar Aderbissanet da ke arewa maso gabashin kasar a cikin halin dimuwa, ganin yadda dabbobinsu ke fuskantar barazanar yunwa saboda rashin ciyawa.

Yadda gobarar daji ta cinye wata gona a gabashin Jamhuriyar Nijar
Yadda gobarar daji ta cinye wata gona a gabashin Jamhuriyar Nijar © Umar Sani/RFI Hausa
Talla

A 'yan tsakanin nan an fuskanci tashin gobara akalla sau 5, abin da ya janyo lalacewar kadada dubu 13 na filin kiwo tare da haddasa asarar abincin dabbobi da ya kai tan dubu 5.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Umar Sani wanda Zainab Ibrahim ta karanta

Maryama,'yar shekaru 50 a duniya, na makwaftaka da inda gobarar dajin ta soma, a wancen rana tace dakyar ta sha.

Kawai dai da ta taso, mun ji tsoronta, tsoron ta muke yi kar mu ma ta cinye mu. Ta cinye mana ciyawa.

In banda guntattakin bishiyoyi marasa amfani ga dabbobi, babu abin da ya rage a Atambo, yankin da al'ummarsa,makiyaya ne.

Ahmed Moussa, matashin makiyayi ya shaida wa RFI Hausa  girman barna da gobarar ta yi wa yankin, yana mai cewa, ba su san irin halin da za su shiga ba saboda rashin ciyawar da suke amfani da ita wajen ciyar da dabbobinsu.

Matashin ya ce, ba su da wani aiki da suke yi na samun kudi da ya wuce kiwo a rayuwarsu, kuma a halin yanzu babu wata hanyar da za su bi wajen samun kudin da za su sayo wa dabbobinsu abinci.

Wani yanki da gobarar dajin ta lakume a gabashin Jamhuriyaar Nijar.
Wani yanki da gobarar dajin ta lakume a gabashin Jamhuriyaar Nijar. © Umar Sani/RFI Hausa

Su ma makiyaya ba su gama farfadowa daga matsalar karancin ruwan sama mai nasaba da sauyin yanayi da aka fuskanta a bana ba abin da Moustapha Kedou, uban iyali, ya ce dole sai gwamnati ta shigo cikin lamarin, yayin da ya ce, babu wanda suka dogara da shi a yanzu sai Allah.

Gobarar wadda ita ce mafi muni da yankin ya fuskanta a tsawon tarihi ta lakume sama da kadada dubu 13 na filin kiwo, yayin da ake dangantaka tashin gobarar da ayyukan da ‘dan Adam da ke yi wa muhalli barna.

Kashi 80% na al'ummar Aderbissanet, yankin da ke a arewa maso gabashin Jamhuriyar Nijar makiyaya ne, saboda haka gobarar daji na zaman baban kalubale ga jama'a, inji Amadou Oumarou Jami'in kula da Ma'aikatar Kiwo a yankin.

Don ceto sama da kilomita 50 na fadin kasar da gobarar ta daidai ta, gwamnati tare da abokan huldarta sun kaddamar da aikin "Sahara Hakki" a yankunan da barnar ta yi wa illa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.