Isa ga babban shafi

Karancin ruwan sama ya haifar da asarar amfanin gona a Nijar

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce an samu karancin ruwan sama a daminar bana, abinda ya kai ga asarar amfani gona da dama.

Wasu manoma a Jamhuriyar Nijar.
Wasu manoma a Jamhuriyar Nijar. © Chris de Bode/Panos
Talla

A jihar Damagaram kadai garuruwa 1079 damanar ta yi wa mummunan kaye.

Rashin ruwan sama ya haddasa rashin ciyawar da dabbobi ke ci a Jihar Maradi, abinda ya kai ga asarar wasu daga cikin dabbobin. 

Wannan ne dalilin da ya sa makiyaya kira ga gwamnati da ta taimaka wajen samarwa dabbobi abinda za su ci domin kaucewa rikici tsakanin manoma da makiyayan. 

Tsaikon ruwan sama da aka samu a ca farkon daminar, ya haddasa fari a cikin gonakin wasu jihohin kasar, inda har ta kai a wasu wuraren yabanyar da ke gonakin ta fara bushewa. 

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Zainab Ibrahim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.