Isa ga babban shafi
Rahoto

Matsalar safarar baki daga Nijar ta dawo bayan hambarar da Bazoum

A Jamhuriya Nijar, fiye da watani uku bayan hambarar da Bazoum Mohamed daga kan kujerar mulki da sojoji suka yi, batun safarar bakin haure da gwamnatinsa ta soke shakaru 8 da suka wuce, na barazanar dawowa gadan-gadan. 

Wasu bakin haure da aka kwashe daga Libya
Wasu bakin haure da aka kwashe daga Libya REUTERS/Hani Amara
Talla

Shakaru 8 bayan gagarumar nasarar da a ka yi wajan dakile kwararar bakin haure da ke son ratsawa ta Nijar don shiga nahiyar Turai, a 'yan tsakanin nan matsalar na kan hanyarta ta dawowa gadan-gadan. 

Bayanai a tashoshin mota da jigilar fasinja na boye na nuni da cewar ana samun karuwar baki daga yammacin nahiyar Afirka da ke son gwada sa'arsu. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Murtala Adamu

'Yan kasashen Burkina Faso da Ivory Cost da kuma Najeriya suka fi kwarara a wadannan  tashoshin mota na boye. 

 Ana daukar kowanne mutum guda ne a kan kudi jaka 200 na CFA daga Agadaz zuwa garin Sabha.

Ofishin Kula da Shige da Ficen Baki a Majalisar Jihar Agadaz, ya bayyana cewa,lamarin na neman subule wa sa'idon mahukunta. 

A cikin wata sanarwa da Hukumar da Bakin-haure ta IOM ta fitar, ta bayyana damuwarta a game da yadda ake samun karuwar bakin 'yan Afirka da Aljeriya da ke kwararowa zuwa Asakama ta Nijar. 

Tsamin dangantaka da ke ruruwa tsakanin Kungiyar Tarayya Turai EU da sabbin mahukuntan soji na Nijar na barazanar dagula al'amurra, inda matasan da suka goyi bayan sojoji ke yawaita kiran a soke dokar, wacce ta yi wa tattalin arzikin jiha illa.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.