Isa ga babban shafi

Ya kamata shugabannin Afrika su fitar da jama'ar Nijar daga kunci - Yayi

Tsohon shugaban Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi, ya bukaci tsoffin shugabannin kasashen Yammacin Afrika da su bayar da tasu gudunmuwa domin warware rikicin da ake fama da shi sakamakon juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar. 

Thomas Boni Yayi
Thomas Boni Yayi AFP - SEYLLOU
Talla

Boni Yayi, ya bayyana wannan fata ne a wata wasika da ya aika wa tsohon shugaban Tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo, inda yake bayyana matukar damuwa a game da halin da jama’a ke ciki na kunci sakamakon takunkumai da kuma tsauraran matakai da kungiyar Ecowas ta dauka a kan Nijar bayan wannan juyin mulki. 

Tsohon shugaban na Benin, ya rubuta wannan wasika ce bayan dawowa daga wata ziyarar gani da ido da ya kai a garin Malanville da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar, inda ya tarar da manyan motoci sama da dubu daya makare da kayayyaki amma aka hana su tsallakawa zuwa Nijar karkashin umurnin Cedeao. 

Lura da hali na matsi da matakan na Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma suka jefa jama’ar Nijar da kuma na Jamhuriyar Benin ne, Boni Yayi ya rubuta wannan wasika zuwa ga Obasanjo inda a ciki yake cewa ‘’

Akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin samar da yanayi na tattaunawa tsakanin Ecowas da kuma mahukuntan Nijar, domin ta hakan ne kawai za a iya ceto jama’a daga matsanancin halin da wadannan takunkumai suka haifar musu’’, 

Tsohon shugaban ya yi fatan takwaransa Obasanjo, zai yi amfani da matsayinsa na tsohon shuguaba kuma mutum mai tasiri a siyasar duniya, domin warware wannan takaddama tsakanin Ecowas da kuma gwamnatin mulkin sojin Nijar. 

A can baya, sau da dama tsohon shugaban na Benin na fitowa fili domin ganin an warware rikicin a diflomasiyance tare da nuna adawa da karfin soji don maido da dimokuradiyya a Nijar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.