Isa ga babban shafi

Motocin agajin abinci sun makale kan iyakar Nijar

Yanzu haka dimbin motoci dauke da kaya mallakin Hukumar Agajin Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato PAM ko kuma WFP, wadanda ya kamata a shigar da su Jamhuriyar Nijar, na ci gaba da kasancewa kan iyakar kasar da Jamhuriyar Benin. 

Wasu motoci da suka makale kan iyakar Nijar
Wasu motoci da suka makale kan iyakar Nijar © Mohammed Babangida / AP
Talla

 

A cewar shugaban Ofishin Hukumar ta WFP a Jamhuriyar Nijar, yanzu haka suna kan yin nazari game da yiyuwar sauya hanya zuwa Burkina Faso don shigar da wannan abinci a Nijar, amma kuma ana fargabar matsalar tsaro a wannan hanya. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken bayaninsa

Jami'in ya ce, kawo yanzu  motocin da aka tsara cewa za su shiga Nijar ko dai daga Najeriya ko kuma Benin ba su samu damar tsallakawa ba. 

Saboda haka duk wani yunkuri na karkata akalarsu domin shiga Burkina Faso, zai kasance abu mai sarkakiya, kuma dole sai an dauki lokaci domin daukar matakai na tsaro da kuma rakiyar wadannan motoci.   Inji shi.

Yau makonni da dama kenan da wadannan motoci dauke da kwantenoni 463 ke can  makale kan iyar Jamhuriyar Benin, yayin da Hukumar Agajin Abincin ke cewa, lalle akwai wasu hanyoyi da za a iya amfani da su, misali daga Kamaru zuwa Chadi kafin a shiga cikin Nijar.   

Sai dai hukumar ta ce, yin hakan ba abu ne mai sauki ba, saboda sai an sake lafta wadannan kaya a kan jiragen ruwa zuwa Douala ko kuma Kribi da ke Kamaru, kuma daga nan a sake sauke su don dorawa a kan motoci, wadanda za su ratsa Kamaru da kuma Chadi kafin shiga Jamhuriyar Nijar.   

Wannan aiki ne mai matukar wuya, saboda za a dauki dogon lokaci, ana bukatar tsaro, saboda haka kafin su isa. Sannan ko shakka babu wannan zai shafi ayyukan jinkai da muke gudanarwa a Nijar. inji WFP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.