Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar 60 - Bayanan sirri

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, na cewa an yi jana’izar jami’an tsaro akalla 60 a jiya Talata a garin Tiliya da ke jihar Tawa kusa da iyakar kasar da Mali, wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar harin ta’addanci a ranar Litinin da ta gabata. 

Sojojin Nijar masu sintiri kan iyakar kasar
Sojojin Nijar masu sintiri kan iyakar kasar US Army/Richard Bumgardner
Talla

Da farko dai Ma’aikatar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta ce dakaru 29 ne suka rasa sanadiyyar harin da ‘yan ta’adda suka kai musu a garin Tabatol da ke kusa da iyaka da Mali, to amma wadanda suka halarci jana’izar wadda aka yi a wannan Talata, sun ce adadin mamatan ya kai akalla 60. 

Bayanai sun ce, wadanda aka yi wa jana’izar, dukkaninsu suna aiki ne a karkashin rundunar zaratan sojoji na musamman da ke fada da ayyukan ta’addanci tsakanin yankin Tiliya mai makotaka da Menaka da ke cikin Mali, kuma sun hadu da ajalinsu ne a hanyarsu ta kai dauki ga wasu jami'an tsaron da ‘yan bindigar suka afka wa. 

Wani abu da ba saban ba, a wannan karo ‘yan ta’addar da ake cewa magoya bayan kungiyar EIGS mai ikirarin jihadi a yankin Sahel, sun shirya kwanton bauna ne ta hanyar dasa abubuwa masu fashewa da kuma yin amfani da motocin da aka makare su da bama-bamai a daidai lokacin da sojojin ke wucewa. 

Daga ranar 26 ga watan Yuli lokacin da sojoji suka yi juyin mulki zuwa yau, masu ikirarin jihadi sun kashe jami’an tsaron kasar ta Nijar da dama a irin wadannan hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.