Isa ga babban shafi

Nijar ta amince wa Aljeriya ta shiga tsakani don magance rikicin kasar

Jamhuriyar Nijar ta amince da shiga tsakanin Aljeriya wadda ta yi wa sojojin da suka yi juyin mulki tayin mika mulki ga farar hula cikin watanni shida.

Shugaban mulkin sojin Nijar,  Abdourahamane Tiani
Shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahamane Tiani © ORTN
Talla

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ma'aikatar Harkokin Wajen Aljeriya ta ce, Nijar ta amince da tayin na shiga-tsakani da zummar lalubo hanyar magance rikicin siyasar kasar.

Tuni shugaban Aljeriya Abdelmajid Teboune ya umarci babban jami'in diflomasiyarsa, Ahmed Attaf da ya yi balaguro zuwa birnin Yamai domin soma tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

A karshen watan Agusta ne, Aljeriya ta gabatar wa Nijar tayin shiga tattaunawar siyasa ta tsawon watanni shida tare da amincewar daukacin jam'iyyun siyasar kasar ba tare da  nuna wariya ba, kuma tattaunawar ta kasance karkashin jagorancin farar hular da kowanne bangare zai amince da ita a kasar.

Manufar shirya wannan tattaunawar ita ce, sake fasalta kundin tsarin mulkin Nijar.

Tun dai lokacin da Aljeriya ta mika wannan tayin, babu wani martani da ya fito daga manyan janar-janar na sojin da ke mulki a Nijar, sai a wannan rana ta Litinin.

Kodayake a ranar 19 ga watan Agusta, shugaban mulkin sojin na Nijar, Janar Abdourahmane Tiani ya bayyana cewa, suna bukatar shekaru uku kafin su mika mulki ga farar hula.

Ana ganin amincewar da sojojin suka yi da tayin Aljeriya, za ta bude kofar shiga tattaunawa da su don lalubo hanyar magance rikicin siyasar kasar.

Fiye da watanni biyu kenan da ragamar mulkin Nijar ke hannun sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum da suka zarga da gazawa wajen samar da tsaro a kasar.

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumai don yi wa sojojin matsin lambar mayar da mulki ga farar hula, yayin da ta yi wa kasar barazanar aike mata da dakaru domin kwato mulkin daga hannun sojojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.