Kamfanoni masu zaman kansu na fuskantar matsalar durkushewa a Nijar
Jamhuriyar Nijar kamar sauran kasashe maso tasowa na nahiyar Afirka na fuskantar durkushewar kamfanoni masu zaman kansu, saboda dalilai daban daban, abinda ke yi wa tattalin arzikinta illa, musamman wajen hana jama’a samun aikin yi da kuma dakile kudaden shigar da gwamnati ke samu da kuma hada hadar kasuwanci.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:05
Yayin da masana ke zargin shugabannin kamfanonin da rashin kwarewa wajen tafiyar da su, wasu masu kamfanonin na zargin gwamnati saboda yawan harajin da ake dora musu da kuma tsadar makamashi.
Salissou Issa ya duba mana lamarin daga Maradi, kamar yadda za a ji a rahotonsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu