Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa - Macron

Shugaban Faransa Emamnuel Macron ya sanar da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa a kasar Sylvain Itte, inda suka hana a kai masa abinda zai ci, sai wanda suke ba shi. 

Shugaban Faranasa Emmanuel Macron
Shugaban Faranasa Emmanuel Macron © Julien de Rosa / Reuters
Talla

 

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai Semur-en-Auxios, inda ya ce an hana kai wa jakadan Faransa dake Nijar abinci a inda ake tsare da shi, sai dai wanda sojoji suke ba shi. 

Wannan na ci gaba da nuna tankiyar da ake samu a tsakanin kasashen biyu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka gudanar wajen hambarar da zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed. 

Kin ficewar jakadan Faranasa a Nijar

Sojojin da suka karbe ikon sun bukaci Jakadan ya fice daga Nijar tun daga watan jiya, amma shugaba Macron ya ce babu inda za shi. 

Macron yace yanzu haka an hana jakadan motsawa da kuma bari a kai masa abinda zai ci. 

Da aka tambaye shi ko Faransa zata dawo da jakadan gida, sai Macron ya ce zai yi duk abinda suka amince da shugaba Bazoum saboda shine halartaccen shugaban da yake magana da shi kowacce rana. 

Zanga-zanga

Magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar na ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da Faransa wadda taki amincewa da juyin mulkin, tare da bukatar janye sojojin ta dake kasar. 

Baya ga Faransa, ita ma kungiyar kasashen Turai ta hannun mai magana da yawun ta Nabila Massrali tace basu amince da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a matsayin halartattun shugabanni ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.