Isa ga babban shafi

Cutar sankarau ta kashe mutane 18 a Nijar: WHO

Majalisar Dinkin Duniya tace wani nau'in cutar sankarau mai tsanani da ya bulla tun cikin watan Nuwambar da ya gabata a Jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18, inda ta yi gargadin cewa annobar na iya yaduwa a yankin. 

Allurar rigakafin cutar Sankaru
Allurar rigakafin cutar Sankaru picture alliance via Getty Image - picture alliance
Talla

Yanzu haka dai Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, tuni aka kaddamar da allurar rigakafin cutar, inda ta tanadi alurai dubu 600 saboda aikin.

WHO ta ce Jamhuriyar Nijar dake fama da cutar ta sankarau a kai akai, sakamakon yadda kasar ke kan layin kasashen nahiyar Afrika dake fama da annobar, da ta ratsa dukkanin nahiya kama daga kasar Sénégal dake yammaci har zuwa Habasha dake gabashi nahiyar. 

Mafi muni

Bayan haka hukumar lafiyar ta ce, annobar da ta  barke a wannan lokaci, ta dara ta kakar da ta gabata yawa.  

Daga ranar 1 ga watan Nuwambar 2022 zuwa 27 ga watan janairun 2023 da muke ciki,  a jimilce mutane 559 ne suka kamu da annobar ta dan sankarau, 111 ne dakin gwaji ya tabbatar, a yayin da 18 kuma suka rasa rayukansu, a jihar Zinder dake kudu maso gabashin kasar ta Nijar. 

(93,7%) na mafi yawan wadanda dakin gwaji ya tabbatar da sun kamu da cutar, sun harbu ne ta sanadiyar kwayar cutar da ake kira Neisseria meningitidis dake cikin rukunin  C (NmC). 

Yankin zinder dai na iyaka ne da jihar jigawa a tarayyar Najeriya, inda yanzu haka ake fama da nau’in kwayar cutar dan sankarau ta  NmC, wanda a cewar Hukumar lafiyar ta MDD ake fuskantar barazanar yaduwarta a duniya 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.