Isa ga babban shafi
Nijar

An gano bama-baman da suka shafe shekaru binne a karkashin wani gida

An gano wata tsohuwar ma’adanar wasu bama-bamai da suka hada da nakiya ta hannu 119 da kuma bam din zamani 38 da aka binne a cikin wani gida da ke unguwar Jagindi a shiya ta 3 ta birnin Damagaram.

Wani yanki na tsohon garin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar.
Wani yanki na tsohon garin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar. © Wikipedia:Hausa
Talla

An gano bama-baman ne a yayin da wani mai hakon rami ke aikin tona masai a cikin wani gida da mutanen ke zaune tsawon shekaru.

Sai bayan da aka gudanar da bincike ne, aka tantance cewa bamabamai ne masu hatsari, lamarin da ya tunzura jama’ar unguwar.

Daga Damagaram wakilinmu Ibrahim malam Tchillo na dauke da rahoto.

01:33

Rahoto kan yadda aka gano bama baman da suka shafe shekaru binne a karkashin wani gida

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.