Isa ga babban shafi

NAFDAC ta garkame shagunan sayar magunguna sama da 1000 a kano

Hukumar dake kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC a Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar masana a fannin sarrafa magunguna ta kasar sun rufe shagunan sai da magunguna dubu 1 da 321 a jihar Kano.Saboda saba ka’ida wajen gudanar da ayyukansu.Hukumomin sunce wasu daga cikin shagunan bas u da rajistar aiki.

Wani shagon sayar da magunguna tarayyar Najeriya.
Wani shagon sayar da magunguna tarayyar Najeriya. Guardian Nigeria
Talla

Daraktan sashin bincike na hukumar ta NAFDAC ne Mr Francis Oninowu, ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ga manema labaru a jihar ta Kano a ranar Litinin, bayan kammala aikin rufe shagunan magunguna dubu daya da 321 a kasuwar sabon gari da Malam Kato da kuma hanyar Niger Street duk a cikin jihar, a tsakanin ranakun 17 da 18 ga wannan wata da muke ciki na Fabrairu.

Daraktan ya kara da cewa sun dauki wannan mataki ne bisa dokar dake kula da tabbacin sayar ingantattun da kuma nagartattun magunguna a cikin al’uma, kuma hakan na kunshe a cikin ka’idoji da sharudda da suke tabbatar da ganin anbisu ba tare da kauce hanya ba.

Ya kuma jaddada bukatar tsaftace tsarin rarraba magunguna a kasar, yana mai cewa idan ba a ajiye magungunan a wurare mau sanyi ba za su gurbace ba.

Oninowu Ya kuma yi nuni da cewa galibin wuraren sayar da magungunan da aka ziyarta suna gudanar da ayyukansu ne a cikin wani yanayi da babu isashiyar iska wacce ake da bukata domin aje magungunan.

Sannan ya kuma bukaci dillalan magunguna da su rika kiyaye wa domin kulawa da lafiya al’uma.

Daraktan ya ci gaba da cewa zas uci gaba da kokarin da suke yin a ci gaba da yaki da magungunan da ba su da inganci a jihar Kano da kuma Najeriya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.