Isa ga babban shafi

Ana fargabar bullar cutar sankarau a Yobe bayan mutuwar dalibai 20

Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu bullar cutar sankarau a wasu makarantun kwana, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla dalibai 20.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni theinterview
Talla

Majiyoyi sun ce an samu bullar cutar ne a makarantun kwana uku a kananan hukumomin Potiskum, Fika da Fune na jihar, wadanda suka hada da ta mata biyu da ta maza daya.

Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Ilimi Dr. Muhammad Sani Idris yayin tabbatar da bullar cutar, ta ce a yanzu haka sauran daliban da suka kamu da ita na karbar magani a asibitin kwararru na jihar da ke Potiskum.

Kazalika, gwamnatin ta ce ta na aiki tukuru domin dakile yaduwar wannan cuta a makarantun da ta bulla da ma a fadin jihar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.