Isa ga babban shafi

Tinubu ya ce a gudanar da bincike kan harin da ya kashe masu Mauludi a Kaduna

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin gudanar da bincike kan harin bom din da rundunar sojojin kasar ta amince ta kai bisa kuskure, kan masu taron Mauludi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi da ke Jahar Kaduna.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. © AP/Gbemiga Olamikan
Talla

A cikin sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a Talatar nan, Tinubu ya jajanta wa iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu game da iftila’in.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya reshen shiyar Arewa maso yamma, ta ce mutane 85 ne suka rasa ransu a hadarin, sannan akwai wasu 66 da ke samun kulawa a asibiti.

Mafi yawan wadanda lamarin ya shafa dai mata ne da kananan yara da kuma dattijai a lokacin da suke gudanar da Mauludi.

Wasu daga cikin wadanda harin sojoji bisa kuskure ya shafa a Kaduna.
Wasu daga cikin wadanda harin sojoji bisa kuskure ya shafa a Kaduna. © Daily Trust

Rundunar sojojin Najeriya na kai mafi yawancin hare-harenta, a yakin da take yi da ‘yan bindiga da kuma masu tada kayar baya a shiyoyin Arewa masu yammaci da kuma Gabashin kasar ta hanyar jiragen sama.

Wannan kuma bashi karo na farko da harin sojojin Najeriya kan fada kan fararen hular da basu ji basu gani ba.

A watan Satumbar shekarar 2021, wani harin sojojin Najeriya bisa kuskure a Kwatar Daban Masara, da ke yankin tabkin Chadi ya kashe Masinta 20 wasu da dama suka samu raunuka.

Haka nan a watan Janairun shekarar 2017, akalla mutane 112 suka mutu a wani hari bisa kuskure shima, da jirgin yakin kasar ya kai a garin Rann da ke kusa da iyakarta da Kamaru.

Ku latsa alamar sauti don sauraron bayanin da mai taimaka wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz.....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.