Rundunar sojin Najeriya ta dauki alhakin harin da ya kashe masu maulidi a Kaduna
A Najeriya gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da tabbacin cewa ko shakka babu jirgin sojin kasar ne ya yi barin wuta kan masu bikin mauludi, a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi, bisa zargin ‘yan ta’adda ne wanda ya kai ga kisan mutane akalla 30.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kunna - 01:30
Tuni dai gwamnatin jihar ta sha alwashin biyan diyyar dukkanin wadanda suka mutu a ibtila’in dama wadanda suka jikkata.
Amma rundunar sojin saman kasar, ta fitar da sanarwar cewa, bata da hannu a harin bam din da ya kashe mutane da dama a kauyen.
Kakakin rundunar, Air Commodore Edward gabkwet, ya lura da cewa basu da masaniya a harin da aka gudanar cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Aminu Sani Sado.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu