Isa ga babban shafi

MSF ta bukaci kara kaimi wajen rigakafin mashako a Najeriya

Najeriya – Kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier tace Najeriya na fuskantar matsalar cutar mashakon da ba’a taba ganin irinsa ba, sakamakon samun mutane sama da dubu 17 da suka harbu da ita, wadda ta kashe akalla 600 daga cikin su.

Un vaccin contre la méningite (photo d'illustration).
Un vaccin contre la méningite (photo d'illustration). picture alliance via Getty Image - picture alliance
Talla

Yanzu haka hukumar lafiya ta duniya da takwararta ta UNICEF sun kaddamar da shirin yin allurar rigakafin cutar a jihohi 14 da suka hada da Katsina da Bauchi da Borno da Kaduna da Kano da Jigawa da kuma Lagos.

MSF tace a jihar Kano kawai cutar ta kama mutane sama da 12,000, kuma kusan kashi 70 na marasa lafiyar da suka je asibitin ta na MSF basu karbi allurar rigakafin ba, abinda ke nuna matsalar rigakafin da ake fuskanta yankin.

Kungiyar tace a fadin jihohin dake yankin arewa maso yammacin Najeriya an samu raguwar masu karbar allurar rigakafin, wanda ya nuna cewar kashi 6 ne kacal suka karbi rigakafin a Sokoto, kashi 10 a Zamfara sai kuma kashi 18 a Katsina, sabanin kashi 36 da aka samu a fadin kasa baki daya.

MSF ta kuma bayyana matukar damuwa da yadda adadin wadanda suka karbi rigakafin ya ragu a jihohin dake arewa maso gabashin Najeriya, ganin yadda kashi 15 ne kacal na marasa lafiyar da aka kula da su a asibitin ta dake Gwange a birnin Maiduguri suka karbi rigakafin.

Yayin da jami’an kungiyar MSF ke karfafa gwuiwar kungiyoyin kasashen duniya da na kasa baki daya dangane da shirin rigakafin, kungiyar ta kuma bukaci kara yawan lokacin da ake dauka domin gabatar da allurar a jihohi da kananan hukumomin Najeriya domin ganin ya kaiga yaran da ake bukata.

MSF tace ta wannan hanyar ce kawai za’a kaiga dakile samun annobar cutttukan da ake iya magance su irin su mashako da kyanda da kuma polio wadanda suke yin sanadiyar salwantar rayuka kowacce shekara.

Kungiyar ta kuma bukaci kungiyoyin bada agaji irin su GAVI da ECHO da kuma Cibiyar yaki da cututtuka na Afirka da su zuba jari a kan ayyukan rigakafi domin magance yaduwar cutar da kuma sake samun wata annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.