Isa ga babban shafi

An rufe manyan asibitocin Gaza biyu saboda hare-haren Isra'ila

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da halin da asibitoci ke ciki a yankin zirin Gaza, inda rohotanni suka ko ranar Asabar manyan asibitocin yankin biyu sun dakatar da aiki, saboda luguden wuta babu kakkautawa da Isra’ila ke yi da kuma matsalar man fetur.

À l'hôpital Nasser de Khan Younès, le 12 novembre 2023.
Wasu Falasdinawa a asibin Nasser da ke Khan Younès. 12/11/23 REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya yi gargadi kan halin da ake ciki na mummunan hadari ga asibitoci a yankin Zirin Gaza, yana mai cewa karin marasa lafiya, ciki har da jarirai da bakwaini na mutuwa.

Manyan asibitocin gaza biyu

Manyan asibitocin Gaza biyu, Al-Shifa da Al-Quds, duk sun rufe, saboda sojojin sari-ka-noken Isra'ila na ci gaba da luguden wuta kan duk wani da suka gani kusa da asibitin Al-Shifa, inda dubban mutane suka makale a ciki.

Ma’aikatar lafiyar Faladinu ta bayyana cewa tun a ranar Asabar janareton asibin na karshe ya daina aiki saboda rashin man fetur, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar bakwaini uku da kuma wasu majinyata hudu. Kuma wasu jarirai 36 na cikin hadarin mutuwa.

Wasu bakwaini a yankin Falasdinawa
Wasu bakwaini a yankin Falasdinawa DR

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya uku sun bayyana firgici game da halin da ake ciki a asibitocin, inda suka ce a cikin kwanaki 36 an samu akalla hare-hare 137 kan cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 521 da jikkata wasu 686 - ciki har da jami’an kiwon lafiya 16 da suka mutu da kuma jikkatar wasu 38.

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare

A halin da ake ciki Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa da kowane kusurwa ciki harda yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, inda rahotanni suka ce an samu fashewar bam a Qalqilya da kuma arangama a Nablus.

Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-haren Isra'ila a Gaza.
Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-haren Isra'ila a Gaza. © KENZO TRIBOUILLARD / AFP

Sojojin Isra'ila biyu ne suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata yayin arangama da mayakan Falasdinawa a yankin Gaza da aka yi wa kawanya, a cewar sojojin Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.