Isa ga babban shafi

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci sake bude kan iyakokin kasar da Nijar

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake bude iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar.

Kan iyakar  Sèmè-Kraké tsakanin Najeriya da Nijar
Kan iyakar Sèmè-Kraké tsakanin Najeriya da Nijar RFI/Jean-Luc Aplogan
Talla

Majalisar ta bukaci gwamnatin kasar ta bude iyakokin Maigatari, Mai’Aduwa, Kongwalam, da Illela.

An zartar da kudurin ne a zaman majalisar na ranar Talata bayan amincewa da kudirin da dan majalisar Kano Aliyu Madaki ya gabatar.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar a watan Agusta, gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokin kasar da na makwabciyarta.

An rufe iyakokin ne biyo bayan takunkumin da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta kakabawa kasar.

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce an rufe iyakokin kasar da Jamhuriyar Nijar ne saboda umarnin ECOWAS na takaita zirga-zirgar kayayyaki har sai an sanar da shi, ba wai domin shelanta yaki ba.

Har ila yau, majalisar dattijai da sauran masu ruwa da tsaki sun bukaci shugaba Bola Tinubu, kuma shugaban kungiyar ECOWAS, da ya dauki matakan diflomasiyya don kawo karshen rudanin siyasar kasar.

Madaki ya gabatar da kudirin, inda ya yi ikirarin cewa garuruwan Maigatari a Jigawa, Kongwalam a Katsina, da Illela a Sokoto manyan kasuwanni ne da ake gudanar da harkokin kasuwanci na kasa da kasa a tsakanin ‘yan Najeriya da mazauna kasashe makwabta kamar Nijar, Mali, Chadi, da Kamaru.

Takunkumin kan iyaka, a cewarsa, ya haifar da wahala mara misaltuwa" ga jama'a da kuma kiyayya tsakanin su da 'yan kasar Nijar.

Sai dai ‘yan majalisar sun nuna adawa da gyaran da aka yi wa kudirin na neman a bude iyakokin kudancin kasar da aka rufe a zamanin tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.