Isa ga babban shafi

Yajin aiki: Gwamnatin Najeriya ta fara amfani da tsarin hana likitoci albashi

Gwamnatin Najeriya ta fara amfani da tsarin “in ba aiki ba biya”, ga mambobin kungiyar likitocin kasar NARD da ke yajin aiki na sai baba ta gani a fadin kasar.

Kungiyar likitocin kasar na zargin gwamnatin da gazawa wajen
Kungiyar likitocin kasar na zargin gwamnatin da gazawa wajen © dailytrust
Talla

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 1 ga Agusta, 2023 da Daraktan tsare-tsare a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Andrew Nuhu, ya sanya wa hannu, kuma aka aika wa manyan daraktocin kiwon lafiya na asibitocin gwamnatin tarayya.

Wasikar ta ce tarurrukan sulhu daban-daban da ma’aikatar lafiya ta tarayya, ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya suka yi da masu ruwa da tsaki na gwamnati, da sakataren gwamnatin tarayya da kuma majalisar dokoki ta kasa, ya gaza shawo kan kungiyar ta NARD ta janye yajin aikin da mambobinta ke yi a fadin kasar.

Kungiyar likitocin kasar ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 26 ga watan Yuli sakamakon gazawar gwamnatin Najeriya wajen biyan likitoci bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.