Isa ga babban shafi

Kungiyar Likitoci a Najeriya ta yi watsi da tayin karin albashi

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ta yi watsi da tayin gwamnatin kasar na karin kashi 25 kan mafi karancin albashin da suke dauka, dai dai lokacin da suka ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani da suka faro a makon jiya.

Ko a farkon watan Mayu sai da likitocin suka yi yajin aikin gargadi kan bukatun da suka gabatarwa gwamnatin.
Ko a farkon watan Mayu sai da likitocin suka yi yajin aikin gargadi kan bukatun da suka gabatarwa gwamnatin. © daily post
Talla

Duk da sanarwar gwamnatin Najeriya kan wannan kudiri, kungiyar ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin wanda ta faro a makon da muke ban kwana da shi, wanda ta ce za ta ci gaba har sai dukkanin bukatunta sun biya.

Bayan wani zama majalisar zartaswar kungiyar likitocin jiya asabar a jihar Lagos, ta bayyana cewa abin da ta bukata shi ne garambawul tare da gyare-gyare a dukkanin Zubin albashin mambobinta ba wai Karin kashi 25 na albashi da biyan wani bangare na kudaden alawus din da likitocin ke bin gwamnati ba.

Sanarwar bayan taro da kungiyar ta fitar ta ce wajibi ne gwamnatin ta mutunta yarjejeniya gyara ga albashin likitocin da aka cimma a shekarar 2009 tare da biyansu dukkanin kudaden alawus din da suke bin gwamnati ba tare tigaciyar wani bangare ba.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban Dr Orji Emeka Innocent da sakataren janar Dr Chikezie Kelechi da kuma sakataren yada labarai Dr Musa Umar ta ce ‘ya’yan kungiyar za su ci gaba da yajin har zuwa lokacin da bukatar za ta biya.

A cewar sanarwar tun farko sun mika dukkanin bukatunsu ga gwamnati tare da bayar da wa’adin shirin tsunduma yajin aikin tun a ranar 5 ga watan Yuli, kuma gaza mutunta bukatun na su ya tilasta musu tsunduma yajin aikin.

Tuni dai wannan yajin aiki ya shafi kusan dukkanin asibitocin Najeriya, wadanda ke fuskantar kamfar likitoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.