Isa ga babban shafi

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ta tsunduma yajin aiki

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 5 a wani yunkuri na tilastawa gwamnatin kasar biya mata wasu daga cikin alkawurran da ta daukar mata tsawon lokaci.

Wasu likitocin Najeriya.
Wasu likitocin Najeriya. © KOLA SULAIMON/AFP
Talla

Da misalin karfe 8 na safiyar yau ne likitocin suka tsunduma yajin aiki a dukkanin sassan Najeriya wanda kuma zai kai su har zuwa nan da ranar litinin mai zuwa don gargadi ga gwamnatin kasar game da wani sabon kudiri da ta gabatar akansu.

Wasu daga cikin bukatun da kungiyar liktocin ke son gwamnati ta biya mata har da karin kashi 200 na albashinsu baya ga janye dokar da ke Shirin tilastawa likitoci aikin akalla shekaru 5 a cikin Najeriya gabanin samun sukunin fita aiki ketare.

Tsawon shekaru likitocin Najeriyar suka shafe suna kai ruwa rana tsakaninsu da gwamnatin kasar game da karin albashi baya ga kyautata yanayin aikinsu ciki har da samar da kayakin aiki na zamani a dukkanin asibitoci.

A lokuta da dama dai kungiyar Likitocin kan shiga irin wannan yajin aikin sai dai kuma bayan shiga tsakani akan shawo kan matsalar, duk da cewa matakin na haifar da mummunar koma baya ga tsarin kiwon lafiya na kasar.

Dubunnan likitocin Najeriya ke tururuwar ficewa ketare don samun rayuwa mai inganci saboda kaucewa tarin matsalolin da bangaren kiwon lafiyar kasar ke fama da shi, duk da yadda kasar ke fama da karancin likitoci.

A baya-bayan nan ne dai Majalisar wakilan Najeriya ta gabatar da wani kudiri da ke neman samar da dokar da za ta haramtawa likitocin Najeriyar ficewa zuwa ketare har sai sun shafe shekaru 5 suna aiki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.