Isa ga babban shafi

Likitoci sun yi barazanar tafiya yajin aiki a Najeriya

Likitoci a Najeriya sun yi barzanar tafiya yajin aiki, idan har gwamnati ta gaza cika musu alkawuran da ta dauka a baya.

Wasu likitoci a dakin tiyata a tarayyar Najeriya
Wasu likitoci a dakin tiyata a tarayyar Najeriya premiumtimesng.com
Talla

Kungiyar likitocin Najeriya a wata sanarwa da ta aikewa ministan lafiya na kasar Dakta Osagie Ehanire, ta ce  za su yanke matakin su ne a babban taronta na kasa da za a gudanar ranar 24 zuwa 28 ga watan janairu.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Dakta Emeka Innocent Orji, ta ce matsawar gwamnatin Najeriya ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa likitoci, babu abin da zai hana su tafiya yajin aikin.

A baya NARD ta bayar da wa'adin watanni shida ga Gwamnatin Najeriya, bisa la'akari da matsalolin da ba a warware su ba da suka shafi mambobinta, ciki har da dambarwar da ta kunno kai game da sake duba asusun horas da ma'aikatan lafiya, na biyan basussukan da ake bin su.

Haka zalika akwai batun alawus alawus da kuma bashin da kungiyar ke bin gwamnati tun daga shekarar 2014, 2015 da 2016, da kuma gaza inganta mafi karancin albashin likitocin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.