Najeriya:‘Yan bindiga sun sace mace mai juna biyu da yarta budurwa a Kaduna
‘Yan bindiga sun sace wata mata mai juna biyu da ‘yarta budurwa a kauyen Akilibu da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Lamarin ya auku ne a daren Asabar da misalin karfe 8 da rabi na dare, inda ‘yan bindigar suka garzaya kai tsaye zuwa gidan wadanda suka sacen.
Jaridar ‘Daily trust’ da ake wallafawa a Najeriya taruwaito cewa ‘ya bindigar ssun isa gidan ne da niyyar sace mai gidan, amma sai suka tafi da matarsa da ‘yarta saboda ba su same shi ba.
Majiyoyi daga kauyen sun ce barayin sun yi ta harbin iska ddon su tsorata mutane a lokakcin da suke aiwatar da aikin nasu.
Wani makawafcin wadanda aka yi awon gaba da su, wanda kuma ba ya so a bayyana ssunansa ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun tafi da matan da ‘yayanta 4, amma daga bisani suka saki yara 3 daga cikinsu.
Har yanzu babu karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, duk kuwa da cewa kakakinta Mohammed jalige, wanda aka tuntuba y yi alkawarin yin hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu