Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun kama masu daukar nauyin 'yan ta'adda a Kaduna

Dakarun a ke aiki a runduna ta musamman ta ‘Operation Hadarin Daji’  sun kama wasu mutane 2 da ake zargin suna dukar nauyin ‘yan ta’adda a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Rundunar ce ta bayyana haka, inda ta ce yaanzu haka ta kaddamar da farautar wani da ake kira Alhaji Abubakar, wanda ake zargin yana taimaka wa ‘yan ta’ada da kudade.

Daraktan yada labaran shelkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a game da nasarorin da runduna ta musamman din ta samu a fadin kasar, daga tsakanin 8 ga watan Satumba zuwa 22 ga watan.

Danmadami ya ce a bankin Access reshen PZ na Zaria ne aka kama wadanda ake zargin a yayin da suke kokarin ciro kudin ya kai Naira miliyan 14, wanda aka saka a cikin asusun ajiya na  Alhaji Abubakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.