Isa ga babban shafi

Sojojin saman Najeriya sun kashe 'yan ta'adda da dama a jihohin Kaduna da Neja

Dakarun rundunar sojin saman Najeriya sun halaka ‘yan ta’adda da dama yayin hare-haren da suka kaddamar kansu a jihohin Kaduna da Neja a karshen mako.

Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya.
Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya. © The Guardian Nigeria
Talla

Yayin taron manema labarai a Abuja, Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce daya daga cikin jiragen yakinsu ya hari ne kan ‘yan ta’addan da ke taruwa a yankin Kurebe da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja, biyo bayan samun bayanan da ke cewa sun hallara a wani muhimmin taro da kwamandan mayakan na Boko Haram mai suna Aminu Duniya, ya shirya.

Aire Commordore Gabkwet ya kara da cewar farmakin ta sama ya yi nasara kashe ‘yan ta’adda da dama, ko da yake ba a san ko jagoransu Aminu Duniya na cikin wadanda suka halakan ba.

Hare-haren da jiragen yakin Najeriya suka kai kan ‘yan ta’adda a yankin Kurebe ya zo ne sa’o’i kadan bayan hadin gwiwar sojojin Najeriya ta sama da na kasa suka kasha wasu ‘yan ta’addar da dama a yankin Damba da Galbi a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya ya ce bayanan sirrin da suka samu sun nuna cewa 'yan ta'addan sun yi shirin mamaye wani kauye da ke kusa da inda suka kafa sansani, abinda ya baiwa sojoji amfani da damar wajen yi musu bazata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.