Isa ga babban shafi
Najeriya-siyasa

Ba za mu yarda da kama-karyar El Rufa'i ba - Sani Sha'aban

Daya daga cikin masu bukatar samun damar tsaya wa Jam’iyyar APC takarar Gwamna a Jihar Kaduna dake Najeriya, Alhaji Sani Sha’aban ya yi watsi da goyon bayan da Gwamna Nasir El Rufai yabai wa Sanata Uba Sani domin zama magajinsa a mukamin Gwamna.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sha’aban ya bayyana goyon bayan  da Gwamnan ya ba Uba Sani a matsayin kama -karyar da ba za su amince da ita ba, lura da cewar ‘yayan jam’iyyar da dama a Jihar Kaduna basu gamsu da matakin da El Rufai ya dauka ba.

Yayin ganawa da manema labarai dangane da matakin da Gwamnan ya dauka na bayyana Sanata Sani a matsayin dan takaran Jam’iyyar ta su a zabe mai zuwa, Sha’aban ya ce kashi 99 na magoya bayan Jam’iyyar APC ba sa tare da El Rufai a kan wannan mataki, wanda zai mayar da wakilan da za su tsayar da ‘dan takarar gwamnan a matsayin marasa amfani.

Sha’aban wanda ya ce shi ya fara sayen fom din tsayawa takarar gwamna a Jihar, ba’a tuntube shi ba domin tsayar da wanda zai yi wa jihar takara duk da zaman sa daya daga cikin masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar, saboda haka ba za su amince da dauki dora ba.

Dan takarar ya ce suna bukatar amfani da dokokin jam’iyya wajen gudanar da zaben fidda gwani domin tsayar da wanda zai yi wa Jam’iyyarsu takara, maimakon kama karya ko tirsasawa ‘yayan jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.