Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

El Rufai ya bukaci daukar matasa dubu guda-guda aikin tsaro daga kananan hukumomi 774

Gwamnan Jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasir El Rufai ya bukaci hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da kuma jihohin kasar 36 wajen daukar matasa dubu guda-guda a kowacce karamar hukuma domin sanya su cikin jami’an tsaron kasar baki daya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

El Rufai ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi rahotan tsaron jihar wanda ke bayyana cewar mutane 830 aka hallaka a cikin watanni 3 da suka gabata, yayin da aka sace dabbobi sama da 1,000 tsakanin watan Yuli zuwa Satumbar da ta gabata.

Gwamnan yace daukar matasa 1,000 daga kowacce jiha zai bada damar samun sabbin jami’an tsaro 774,000 a kananan hukumomin kasar 774 wadanda zasu taimakawa jami’an tsaron da ke aiki yanzu haka wajen  tinkarar matsalolin tsaron da suka addabi kasar baki daya.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng

El Rufai yace yayin da wannan shiri zai taimaka wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya, zata kuma bada damar murkushe masu aikata laifuffukan da suka hana kasar zaman lafiya.

Gwamnan ya bukaci mazauna jihar Kaduna da su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin su, yayin da ya bayyana cewar gwamnatin sa zata ci gaba da daukar matakan da suka dace wajen kare lafiya da dukiyoyin su.

El Rufai ya kuma aike da sakon ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwan su, tare da jami’an tsaron da suka rasa rayukan su yayin da suke kokarin kare lafiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.