Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Aminu ya maka El Rufai kotu saboda sarautar Zazzau

Daya daga cikin fitattun masu rike da sarautar gargajiya Masarautar Zaria, wato Iyan Zazzau Bashir Aminu, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya, Malam Nasir El Rufai kotu saboda abin da ya kira kauce wa ka’ida wajen nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar, yau Litinin lauyoyin Iyan Zazzau suka shigar da kara a babbar kotun Kaduna, inda suke bukatar ta da ta bayyana shi a matsayin halartaccen Sabon Sarki saboda shine ya samu kuri’un da suka fi yawa lokacin da masu zaben Sarki suka kada kuri’a.

Jaridar ta ce takardar karar da ta samu ta nuna cewar cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotun bayan Gwamna El Rufai, akwai kwamishinan shari’a na Jihar Kaduna da Majalisar Sarakunan Jihar da Masarautar Zazzau da Wazirin Zazzau Ibrahim Aminu da Fagacin Zazzau Umaru Muhammad da Makama Karamin Zazzau Mohammed Abbas da Limamin Juma’an Zazzau, Dalhatu Kasimu Imam da Mohammed Sani Aliyu, Limamin Konan Zazzau da Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli sabon Sarki.

Takardar karar ta bukaci bayyana Iyan Zazzau a matsayin Sabon Sarki da kuma soke nadin da aka yiwa Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau.

Takardar karar ta kuma bukaci kotun da ta dakatar da duk wani yunkuri na bikin nada Ahmed Bamalli da bashi sandar girma da gwamnatin jihar Kaduna ko wani jami’in ta zai yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.